Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar aiki birnin Malabo na kasar Equatorial Guinea, a ranar Laraba.
Fadar Shugaban Kasa ta ce a yayin ziyarar aiki na kwana uku, Tinubu da Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, za su tattauna kan harokin mai da kuma tsaro.
Sanarewar da hadimin shugaban kasa, Ajuri Nglale ya fitar ta ce, Ministan Harkokin Waje, Ambasada Yusuf Tuggar, zai kasance a tare da shugaban kasa a ziyarar, inda za su sa hannkun kan yarjejeniya tsakanin kasashe biyu.