Shugaban Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, na shirin tsawaita wa’adin mulkinsa bayan shafe shekara 43 yana shugabancin kasar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke shirin gudanar da babban zabenta a Lahadi mai zuwa.
- ’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Zamfara
- Tir da masu amfani da tabar wiwi a girke-girke —Marwa
‘Yan kasar dai na alakanta mulkin Teodoro Obiang da kama-karya da rashawa, inda suke fatan kawo karshen gwamnatinsa a zabe mai zuwa.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, a yanzu duk duniya Obiang ne Shugaban Kasa mafi dadewa kan karagar mulki, wanda ya shafe shekara 43 yana mulki.
A tarihin kasar, shuganni biyu kacal aka taba samu tun bayan samun ‘yancin kai da ta kasar ta yi daga gwamnatin Sfaniya a 1968 – Obiang da kawunsa Francisco Macias Nguema, wanda ya yi wa juyin mulki a 1979.
Kafin wannan lokaci, duka zabukan da aka yi a baya, Obiang mai shekara 80 ne yake lashewa.
Lamarin da ya sanya masu sanya ido kan harkokin zabe daga kashen waje suka diga ayar tambaya kan takarar da dattijon zai yi karo na shida.
Equatorial Guinea kasa ce mai arzikin mai wadda yawan al’ummarta bai wuce kimanin miliyan 1.5 ba.