Rundunar ’Yan Sandan Jihar Benuwe, ta kashe wasu ’yan bindiga shida a wani samame da ta kai sansaninsu da ke Unguwar Mbavuur a Ƙaramar Hukumar Logo a jihar.
Rundunar Operation Zenda JTF ta samu bayanan sirri kuma tare da kai hari, inda ta kashe ’yan bindigar.
- Za mu bai wa masu zanga-zanga kariya —Shugaban ’yan sanda
- Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin sayar wa Dangote ɗanyen mai
Wasu daga cikinsu ’yan bindigar sun tsere, kuma ’yan sanda na ci gaba da bin sahunsu.
Kazalika, jami’an rundunar sun ƙwato makamai, ciki har da bindigar ƙirar AK-47.
Har wa yau, rundunar ta kama ɗan fashin da ya addabi a hanyar Makurdi zuwa Lafia, Tersoo Dabo.
Bayan yi masa tambayoyi, ya amsa cewar yana cikin wata tawaga mai mutum bakwai.
Bincike ya kai ga kama Martin Akunu, wanda ake zargin shugaban ƙungiyar asiri ce.
Rundunar ta ƙwato makamai da alburusai da dama a wajensu.
A ranar 28 ga watan Yuli, ’yan sanda sun kama Usman Hardo, wanda ake ruwa a jallo kan zargin sace mutane da shanu a Jihar Nasarawa.
Rundunar ta yaba wa jama’ar jihar, kan goyon bayansu, inda ta tabbatar musu da cewar za ta ci gaba da ba su kariya.