Jami’an rundunar ’yan sandan Jihar Ribas sun harbe wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka addabi yankin Oyigbo-Igbo-Etche na Jihar.
Kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko ta bayyana hakan a wata sanarwa.
A cewarta, ’yan sanda da ke aiki da sashen leken asiri na rundunar sun kai farmaki maboyar masu garkuwa da mutane a dajin Oyigbo-Igbo-Etche, inda suka yi artabu da ’yan bindigar da suka dauki tsawon sa’a guda.
Sanarwar ta bayyana cewa shugaban kungiyar, mai suna Blacky, ya samu rauni sosai yayin da aka harbe wani Peter Nwafor a lokacin da yake kokarin tserewa.
An kai mutanen biyu zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Fatakwal, inda aka tabbatar da mutuwarsu tare da ajiye gawarwakinsu.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa ’yan kungiyar na da alaka da sace wata mata da diyarta a ranar 18 ga watan Maris, 2023 a Fatakwal.
Abubuwan da aka gano a wurin da lamarin ya faru sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya da harsashi 18.