Rundunar ’yan sandan Najeriya ta gano sandar majalisa da wasu ’yan daba biyar suka sace yayin da ’yan majalisar ke yin zama a zauren majalisar ranar Larabar da ta gabata.
Mataimakin Mai Magana Da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, SP Aremu Adeniran a sanarwar da ya fitar da safiyar yau Alhamis ya ce an gano sandar da aka sace a majalisar a karkashin gadar da ke daf da kofar shiga garin Abuja.
Aremu ya bayyana cewa Sufeto Janar na ’yan sanda, Ibrahim Idris ya dauki matakin gaggawa inda ya ummarci rundunar ’yan sanda da ke bincike na musamman karkashin jagorancin Sefeto Janar da ke sanya sanya ido su nemo sandar cikin gaggawa. Tare da kama ’yan dabar.
Aremu ya bayyana cewa Sufeto Janar na ’yan sanda ya bayar da ummarnin rufe birnin tarayya na Abuja tare da tsaurara matakan tsaro da sanya ido ta hanyar binciken motoci a inda ’yan sanda ke binciken motoci don gano wadanda suka sace sandar tare da kama su.