Kwamishinan Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja Benneth Igweh, ya bayar da umarnin fara binciken kan kisan da wasu da ake zargi ‘yan fashi suka yi wa wani tsohon ɗin Janar a gidansa da ke Abuja.
Maharan sun kutsa gidan Birgediya Janar Uwem Udokwere (mai ritaya), inda suka yi masa kisan gilla.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 7 a wani sabon hari a Katsina
- Yadda dangantakar ɓangaren zartarwa da majalisa ta kasance daga 1999 zuwa 2024
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Josephine Adeh ta fitar, ta ce an kashe tsohon janar ɗin a gidansa da ke rukunin gidajen Sunshine da ke unguwar Lokogoma a eanar Asabar.
Kwamishinan ya kuma jajanta wa iyalan marigayin, tare da yin alƙawarin farautar waɗanda ke da hannu a kisan nasa.
‘’Za mu yi duk abin da ya dace don tabbatar da kama maharan domin gurfanar da su a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka,” in ji sanarwar.
Aminiya ta ruwaito yadda wasu ’yan fashi da makami sun kashe Janar ɗin a gidansa.