’Yan sanda sun far wa ’yan jaridar kafofin yada labaran Daily Trust da takwaransa na BBC a yayin da suka ke daukar rahoto a kotun sauraron kararrkin zaben gwamnan Kano, wadda a yau za ta yanke hukunci.
Zahraddeen Lawa na BBC da Salim Umar Ibrahim na Daily Trust sun fuskanci hakan ne daga ’yan sandan da aka girke a wurin da kotun za ta yi zaman.
- Nadin Hakeem Baba-Ahmed ya nuna Tinubu ya shirya yin aiki
- Yau kotu ke yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano
Da farko ’yan sandan sun umarci ’yan jaridar su yi nesa da baya da kimanin mita 10.
Ana cikin haka ne waus daga cikin jamia’n tsaro suka fara cin mutuncin ’yan jaridar, wai suna daukar hoto.
’Yan sandan sun yi cakumi wakilin BBC suna kokarin kwace wayasa daga aljihunsa,a yayin da wasu suka nemi kwace wayar takwaransa na Daily Trust, inda a garin haka suka fasa fuskar wayar.