Rundunar ’yan sandan Kano ta sake dawo da dokar hana yin taruka ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Asabar.
- Dalilin rushe Majalisar Zartaswar Jihar Bauchi — Bala Mohammed
- Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta yi sabbin nade-nade
A cewar Kiyawa, Kwamishinan ’yan sandan Kano, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya dawo da dokar ce bayan zama da ya yi da manyan jami’an tsaro a jihar.
“Sun tattauna kan yadda za a bullo da hanyoyin samar da tsaro tun kafin ranar da kuma bayan Ranar Dimokuradiyya.
“Ya bayyana cewar an hana taruka wanda ba bisa ka’ida ba a fadin jihar.
“Duk wanda aka samu yana kokarin ta da fitina ko zaune tsaye, za a kama shi tare da hukunta shi nan take,” cewar Kiyawa.
Kazalika, Kiyawa ya ce Kwamishinan ya gana da shugabannin sassa na rundunar ta Kano kan su zage damtse wajen wanzar da zaman lafiya a jihar.
“A yayin tattaunawar ya umarce su da su ci gaba da maida hankali wajen zakulo maboyar bata-gari a fadin jihar tare da gurfanar da su,” in ji sa.
Haka kuma, Kwamishinan ya yaba wa gwamnatin Kano da jama’arta, Sarakunan gargajiya da kafofin watsa labarai da sauransu kan yadda suke taimakon rundunar ’yan sandan wajen gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Shi ma Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyin bangar siyasa.
Aminiya ta ruwaito cewa, wannan mataki na rundunar ’yan sandan jihar na zuwa ne awanni kadan bayan gangami da jam’iyyar APC a jihar ta yi wanda ya rikide zuwa rikici.