✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun dakile wani hari kan matatar Dangote

’Yan sandan sun sanar da dakile harin da aka kai matatar mai ta Dangote.

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da dakile wani hari da wasu mutane suka yi kokarin kaiwa matatar tace man fetur na kamfanin Dangote da ke Jihar Lagos.

Wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Benjamin Hundeyin ya gabatar ta ce wasu mutane akalla 20 ne suka kutsa kai cikin kamfanin ta cikin teku da asubahin Litinin.

Ya ce mutanen mutanen da suka kutsa kai cikin matarar man sun yi kokarin kwashe wasu kadarorin da ke ciki, kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su.

Jami’in yace jami’an tsaro sun yi nasarar harbe mutum guda daga cikin barayin, kuma ya mutu lokacin da ake kokarin kai shi asibiti.

Hundeyin ya ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Abiodun Alabi ya ba da umurnin kara matakan tsaro a matatar.

%d bloggers like this: