Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da dakile wani hari da wasu mutane suka yi kokarin kaiwa matatar tace man fetur na kamfanin Dangote da ke Jihar Lagos.
Wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan, Benjamin Hundeyin ya gabatar ta ce wasu mutane akalla 20 ne suka kutsa kai cikin kamfanin ta cikin teku da asubahin Litinin.
- Muna takaicin hargitsin da aka tayar a filin wasa na Abuja —NFF
- Nakasassun ‘yan mata sun koka kan rashin samun mazan aure
Ya ce mutanen mutanen da suka kutsa kai cikin matarar man sun yi kokarin kwashe wasu kadarorin da ke ciki, kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su.
Jami’in yace jami’an tsaro sun yi nasarar harbe mutum guda daga cikin barayin, kuma ya mutu lokacin da ake kokarin kai shi asibiti.
Hundeyin ya ce Kwamishinan ’yan sandan Jihar Legas, Abiodun Alabi ya ba da umurnin kara matakan tsaro a matatar.