✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun dakile harin ’yan fashi a Kaduna

'Yan sandan sun kwato makamai da motar da aka yi yunkurin fashi da ita.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ce jami’anta sun dakile wani harin ’yan fashi tare da kwace makamai da motar ’yan fashin a Jihar.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar, ASP Mohammaed Jalige ne ya tabbatar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Litinin a Kaduna.

  1. Rabon mukamai: Buhari bai mayar da ’yan kabilar Ibo saniyar ware ba – Ngige
  2. Mutumin da ya fi kowa yawan iyalai a duniya ya kwanta dama

Ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar 13 ga Yunin 2021 a kan Titin Jada Road da ke unguwar Tudun Wada a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu.

ASP Jalige ya kuma ce, “Nan take wasu jami’an ’yan sanda suka kai dauki yankin.

“Kwararrun jami’an sun yi nasarar rarakar ’yan fashin tare da dakile yunkurin nasu,” inji shi.

Jalige ya ce jami’an tsaron sun kuma sami nasarar kwato manyan harsasai guda 24, sai kananan harsasai da dama da kuma kananan bindigu guda 12.

Kazalika, ya ce an kwace motar da suka yi yunkuri yin fashin da ita kirar Toyota Corolla LE ruwan toka mai lambar ABJ 704 MX, tare da katin shaidar tuki da kuma katin cirar kudi (ATM).

Kakakin, ya shaida cewar wasu daga ’yan fashin sun tsere bayan samun raunuka da suka ji yayin artabu da jami’an ’yan sanda.

“Ana bukatar samun bayanin duk wani wanda aka gani da raunin harsashi a jikinsa ga ’yan sanda,” inji Jalige. (NAN)