’Yan sanda sun yi nasarar dakile wani harin ’yan bindga a Karamar Hukumar Tsafe da ke Jihar Zamfara.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ayuba El-Kana ne ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai a Gusau, a ranar Laraba.
- An harbe mutum 2, an sace ma’aikatan lantarki ’yan China 3 a Neja
- Za a fara yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa a Filato – Lalong
“A ranar 4 ga watan Janairu ne dakarun ’yan sanda na musamman da aka ajiye a kan titin Gusau, Tsafe da Funtua suka samu wani kira a lokacin da suke sintiri, cewa an hangi wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai suna kokarin kai hari.
“’Yan bindigar sun tare hanyar tare da sace mutane, suka gudu da su zuwa maboyarsu a Dajin Mutu da ke Karamar Hukumar Tsafe.
“Bayan samun wannan kira ne muka tura jami’an namu suka bazu a cikin dajin inda aka yi dauki-ba-dadi tsakaninsu da ’yan bindigar,” kamar yadda ya bayyana.
Kwamishinan ya kara da cewa ’yan sandan sun fatattaki ’yan bindigar har suka raunata biyu daga cikinsu sauran kuma suka tsere da muggan raunukan harbi.
Daga cikin kayayyakin da aka gano a wajen ’yan bindigar akwai harsasai 22 da babur din hawa daya da wayar salula kirar ‘Tecno’ guda biyu.
Kwamishinan ya jinjina wa jama’ar Jihar Zamfara kan yadda suke taimaka wa jami’an tsaro da bayanai, wanda a cewarsa yake haifar da kyakkyawan sakamako.