✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun daƙile satar mutane, sun kama wasu 3 a Borno

Jami'an tsaro sun bi bayan 'yan bindigar, inda suka cafke wasu uku daga cikinsu.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu.

Majiyoyin tsaro sun shaida wa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan Fabrairu da misalin karfe 1 na dare.

Wasu ’yan bindiga huɗu suka kai hari gidan Mohammed Abubakar, mazaunin Sabon Gari Lassa, da nufin sace shi.

“Wanda suka yi niyyar sacewa ya yi ƙoƙarin kare kansa da adda, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa ba tare da sun cimma burinsu ba”, in ji majiyar.

Bayan haka, Abubakar, ya gaggauta kiran ’yan sanda, inda tare da haɗin gwiwar ’yan banga, jami’an tsaro suka bi sahun ’yan bindigar zuwa maɓoyarsu.

A sakamakon haka, rundunar ‘yan sanda ta cafke mutum uku da ake zargi, dukkaninsu mazauna ƙauyen Gajali da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba.

“Haka kuma an ƙwato wata bindiga da aka ƙera a gida daga hannun waɗanda ake zargin,” in ji majiyar.

Rundunar ’yan sandan jihar, ta yaba da yadda jami’an tsaro suka mayar da martani cikin gaggawa, tare da yin kira ga al’umma da su kasance masu lura da duk wani abu da ba su saba gani ba.

Ta kuma buƙaci su gaggauta kai rahoto ga jami’an tsaro domin ɗaukar mataki a kan lokaci.