Rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara ta ceto wasu mutum tara da suka hada da mata bakwai da maza biyu da aka yi garkuwa da su ranar Talata a kauyen Kucheri da ke Karamar Hukumar Tsafe ta jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Mohammed Shehu Anipr, ya ce an samu nasarar ceto mutanen ne bayan wasu sahihan bayanai da suka samu daga wani basarake.
- Yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada —Sheikh Ibrahim Khalil
- Gwamnati za ta binne gawarwaki 49 a rami guda a Kaduna
CSP Shehu, ya ce wadanda ake ceto an kai su asibitin ‘yan sanda da ke Gusau, inda aka duba lafiyarsu kafin daga bisani jami’an tsaro suka sada su da ‘yan uwansu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Kolo Yusuf ya taya jami’ansa murnar nasarar da suka samu na ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Ya kuma tabbatar wa jama’a yadda suke ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.