✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun ceto mutum 4 da aka sace a Enugu

'Yan sandan sun tsere sun bar mutanen da suka sace, bayan matsin lamba daga 'yan sanda.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Enugu ta ceto wasu mutum hudu da aka yi garkuwa da su a Dajin Akama-Oghe da ke Karamar Hukumar Ezeagu a jihar.

Wannan na dauke ne cikin sanarwar da kakakin ’yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe, ya fitar a ranar Lahadi a Enugu.

“An ceto maza uku da mace daya a Dajin Akama-Oghe wadanda aka sace a ranar Juma’a da misalin karfe 8 na dare a yankin.

“’Yan sanda sun gano wata mota kirar Marsandi wadda mallakim daya daga cikin wadanda aka sace ce, bayan kubutar da su an sake sada su da iyalansu,” a cewarsa.

Ndukwe, ya ce sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan samun bayanan sirri daga jama’ar yankin.

Kakakin, ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar, Ahmed Ammani, ya ba da umarnin bankado inda maharan suka shiga.

Ya ce ’yan bindigar sun tsere sun bar wadanda lamarin ya rutsa da su, bayan da suka fuskanci matsin lamba daga rundunar ’yan sandan jihar.