✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto mutum 3 daga hannun ’yan bindiga a Nasarawa

An sace mutanen ne a kan hanyar Kaduna zuwa Keffi.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, sun kai samame maɓoyar masu garkuwa da mutane tare da ceto mutum uku a Ƙaramar hukumar Karu.

Waɗanda aka ceton su sun haɗa da Abdulsalam Shuaibu, Sani Shuaibu, da Blessing Okorie, waɗanda aka sace a kan titin Kaduna zuwa Keffi.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce maharan sun tafi da su zuwa daji.

Bayan samun rahoton, SP Zaks Wambai, DPO na yankin, ya jagoranci tawagarsa don yin bincike.

Tawagar ta gano maɓoyar maharan inda suka fatattake su, tare da ceto waɗanda aka sace.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Nasarawa, CP Shetima Jauro Mohammed, ya yaba wa jami’an kan nasarar da suka samu.