Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta ceto wasu matafiya 48 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
A cewar ’yan sandan, har yanzu wata mace guda daya na hannun maharan.
- Najeriya A Yau: Anya magoya baya za su bari Ganduje da Kwankwaso su daidaita?
- An sace mutum 4 suna sallah a Taraba
Hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, ASP Jalige Mohammed ya fitar a yammacin ranar Alhamis.
Aminiya ta rawaito a ranar Laraba cewa ’yan bindiga sun kai farmaki a kan hanyar Birnin Gwari tare da sace mutane da dama duk da cewar suna tare ’yan sanda
ASP Jalige, ya ce rundunarsu ta yi nasarar tseratar da mutum 48 tare da raka su zuwa inda za su je.
“Kokarin da ’yan sanda suka yi ya sa maharan guduwa su bar mutanen da suka yi garkuwa da su, inda da yawansu suka samu rauni,” a cewarsa.
Ya ce za su kara kaimi don tabbatar da ceto macen da ta rage a hannun ’yan bindigar, sannan za a baza jami’an tsaro don kwaso kayan matafiyan da suka bari a hanya.
Kazalika, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, ya jinjina wa jami’an tsaron kan yadda suke fuskantar ’yan bindiga don tabbatar da samuwar tsaro a jihar.
Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin haske game da rahoton da ke cewa ’yan bindiga sun sake kai hari kan matafiya a kan hanyar a ranar Alhamis ba.