Akalla matafiya hudu ne suka shaki iskar ‘yanci bayan da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Osun ta ceto su daga hannun wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da su a yankin Ere-Ijesa.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar CP Wale Olokode ne ya baza kwararrun jami’an tsaron da suka ceto matafiyan bayan shigar da rahoton batansu.
Kwamishinan, wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, Misis Yemisi Opalola, ya ce sun samu taimako daga wajen wasu jami’an tsaron yayin ceto matafiyan.
Sai dai ya ce daya daga cikin jami’an tsaron ya rasu a bakin daga lokacin da ake kokarin kubutar da matafiyan daga hannun ‘yan bindigar.
CP Olokode ya kuma ce ‘yan sanda za su ci gaba da fadada dabarun yaki da ta’addanci a jihar, don samar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Kazalika, ya bukaci hadin kan jama’ar jihar ta fuskar taimakawa da bayanan duk wani bata-gari don gurfanar da shi gaban doka.