✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun yi garkuwa da hafsoshin soji 7

’Yan sanda sun kubutar da hafsoshin soja biyar daga hannun ’yan bindiga

’Yan bindiga sun yi garkuwa da hafsoshin sojin ruwa bakwai a yankin Kudu maso Kudu a Najeriya.

An yi awon gaba da wasu hafsoshin sojin ruwan ne a Jihar Edo yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Jihar Delta daga Kaduna.


Wata majiya ta ce wadannan hafsoshin sojin ruwa da aka yi garkuwa da su sun taso ne daga sansaninsu Sojin Ruwa da ke Jihar Kaduna, “Suna a kan hanyarsu ta zuwa Kwalejin Injiniyan Rundunar Sojin Ruwa da ke Sapele a Jihar Delta”.

Aminiya ta samu rahoto cewa ’yan sanda sun yi nasarar kubutar da biyar daga cikin hafsohin sojin bayan ’yan bindigar sun yi gakuwa da su a kan hanyar Sapele-Warri. Har yanzu ana neman mutum biyun da suka rage.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jjihar Edo, SP. Kotongs Bello, ya tabbatar da rahoton amma bai yi cikin cikakken bayani ba.

Ya ce, “Mun kubutar da mutum biyar kuma har yanzu ba a kubutar da wasu biyu ba. Wannan shi ne abin da na sani.”

A yanzu haka Najeriya na fama da babbar matsalar rashin tsaro kuma jami’an tsaro ba su tsira ba.

Kasa da mako biyu ke nan da ’yan bindiga suka kashe wani Janar din sojin kasa a Jihar Kogi, a Jihar Zamfara kuma suka harbo jirgin soji, amma matukin jirgin ya tsallake rijiya da baya.

A kwanan nan ne kungiyar ISWAP ta fitar da hotunan wasu sojoji da ake zargin ta yi garkuwa da su a Jihar Yobe.

A lokuta da daban-kuma kuma ’yan bindiga sun sha yin garkuwa da jami’an ’yan sanda a baikin aikinsu.