’Yan Sandan a Jigawa ta ceto wani mutum mai shekara 50 da aka yi garkuwa da shi, Musa Barma, a Karamar Hukumar Malam-Madori.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ya fitar ranar Talata.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sabuwar Dokar Zabe Za Ta Hana Magudi A 2023
- Gibin kudin shiga ke gurgunta wutar lantarki a Najeriya —APGC
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 2:30 na rana, inda wasu ’yan bindiga suka kai farmaki gidan Musa Barma suka yi awon gaba da shi.
Ya ce bayan samun labarin, ’yan sandan sun gano su, suka yi musu kwanton bauna a kan hanyar da ’yan bindigar suka bi a kusa da kauyen Arbus a Karamar Hukumar Kaugama.
Ya bayyana cewa, sakamakon musayar wuta da ’yan bindigar, ‘yan sanda, sun yi nasarar ceto wanda aka yi garkuwa da shi ba tare da ya ji rauni ba, yayin da maharan suka tsere zuwa cikin daji.
Shiisu, ya ce an kama mutum daya mai suna Nura Ahmad a unguwar Abuja a Karamar Hukumar Malam Madori wanda ake gudanar da bincike a kansa.
Ya ce an mayar da binciken lamarin zuwa hedikwatar SCIID domin gudanar da bincike mai zurfi.