An kama wasu ’yan haramtacciyar kungiyar IPOB dauke da bindigogi a yayin musayar wuta da jami’an tsaro.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ebonyi, DSP Loveth, ta ce ’yan sanda sun cafke mutum shida ’yan IPOB din da bindigogi kirar hannu guda biyar da kunshin harsashi guda 12.
- ’Yan ina-da-kisa sun hallaka shugaban hukumar NECO
- Za mu kamo masu garkuwa da daliban Islamiyya — Gwamnatin Neja
“Bata-garin suna hango ’yan sanda sai suka bude musu wuta.
“An harbi biyu daga cikinsu a yayin artabun, ragowar kuma suka tsere da raunukan harbi zuwa cikin daji,” kamar yadda ta bayyana a ranar Talata.
Odah ta ce an kame ’yan kungiyar IPOB din ne a ranar Litinin yayin da suke tailasta wa mutane zaman gidan a Jihar ta Ebonyi.
Ta ce an kwace makamai a wurin wadanda ake zargin da suke amfani wajen aikata ta’addanci.
“Sun kone mota kirar Toyota tare da babura guda biyar.
“Sun farmaki mutanen da suka amincewa da umarnin zaman gidan da IPOB ta bayar.
“An Kai wadanda suka samu rauni a harin na IPOB Asibitin Koyarwa na Alex Ekwueme, don ba su kulawa,” a cewarta.
Kazalika, ta ce an sake cafke wasu mutum biyu ’yan IPOB kusa da hedikwatar ’yan sandan jihar.