✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke ’yan jagaliya 61 a taron Tinubu a Kano

Kakakin ya ce rundunar ta cafke ’yan daban a wajen gangamin yakin neman zaben Jam'iyyar APC a jihar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke ’yan daba 61 a wajen taron yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne, ya sanar da hakan a ranar Alhamis.

“Mun kwato wukake 33, lauje takwas, tabar wiwi, kwaya da sauran kayan maye a hannunsu,” in ji shi.

Kiyawa ya ce hakan na daga cikin shirin rundunar na ganin an yi zaben da ke tafe lafiya, tare da kawo karshen ayyukan ’yan daba a jihar.

Ya ce da zarar rundunar ta kammala bincike a kansu za ta mika su kotu don yanke musu da hukunci.

A baya-bayan nan dai ayyukan ’yan daba sun kara kamari a Jihar Kano bayan fara yakin neman zaben ’yan siyasa.

A ranar Laraba ne dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya kaddamar da yakin neman zabensa a jihar.

Sai dai an yi zargin cewar ’yan daba sun ci karensu ba babbaka.