✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke wani da kokon kan mutum a Ondo

Za a mika masu laifin zuwa kotu don yanke musu hukuncin da ya dace.

Jami’an tsaro a Jihar Ondo sun cafke wani mutum dauke da kan mutum a cikin buhu.
Mutumin ya shiga hannun ’yan sanda ne a ranar Alhamis, a yankin Ajagbale da ke Ondo, dauke da kan mutum a cikin buhu.
A cewar ’yan sandan, bayan gudanar da bincike mutumin ya amsa cewa ya samo kan mutumin ne saboda yana so ya yi tsafi da shi domin ya yi arziki.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Oyeyemi Oyediran, ya ce sun yi nasarar sake cafke wani mutum bayan samun wasu bayanan sirri, cewa mutumin ya dauki budurwarsa zuwa otal wanda a nan ne ya kashe ta tare da datse mata kai.
An cafke wanda ake zargin ne a yayin da yake kokarin tserewa daga otal din a ranar 17 ga watan Disamba 2021.
Bayan cafke shi an shiga dakin da ya datse kan matashiyar inda aka same ta cikin jini a kwance.
Kwamishinan ya ce tuni aka fara  gudanar da bincike kafin mika su zuwa kotu.