✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun cafke Muhuyi Magaji Rimingado a Abuja

Muhuyi ya shiga hannu a masaukin gwamnan Sakkwato da ke Abuja.

Tawagar wasu jami’an ’yan sanda ta cafke tsohon shugaban Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Cin hanci da Rashawa na Jihar Kano (KPCACC), Muhuyi Magaji Rimin Gado.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, an cafke Muhuyi ne a masaukin gwamnan Sakkwato da ke Abuja, inda ya je domin a tantance shi a matsayin daya daga cikin manema takarar kujerar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP.

Bayanai sun ce ’yan sandan sun tisa keyar Muhuyi jim kadan bayan kammala tantance shi, inda suka ka garzaya da shi ofishinsu da ke babban birnin kasar.

Wata majiya ta ce za a mayar da shi Jihar Kano domin ya fuskanta zarge-zargen da ake tuhumarsa da su.

Aminiya ta ruwaito cewa, tuna watan Yulin bara ce Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Barista Muhuyi Magaji saboda kin karbar sabon akantan da Akanta Janar na Jihar Kano ya tura wa hukumar.

Dakatarwar, wacce ta fara aiki nan take tun a wancan lokaci, ta biyo bayan samun  takardar  korafi da Majalisar ta yi daga Ofishin Akanta Janar din ne a kan lamarin.

Tun da farko dai Majalisar Jihar ta aike da goron gayyata ga Muhuyin kan ya bayyana a gaban kwamitin da ta kafa don binciken zarge-zargen da ake masa ranar Laraba, 14 ga watan Yulin 2021.

To sai dai ya gaza bayyana a gaban kwamitin inda ya fake da cewa ba shi da lafiya har ma ya hada da kwafin takardun Asibitin Kasa, wanda hakan ne ya sa majalisar ta nemi tabbatar da sahihancin takardar daga asibitin.

Asibitin Kasa da ke Abuja ya ce takardar rashin lafiyar da Muhuyin ya gabatar wa Majalisar Dokokin Jihar Kano kan lafiyarsa ta bogi ce.

Kazalika, asibitin ba wai kawai ya bayyana cewa takardar ta bogi ba ce, ya kuma ce ba shi da kowanne irin bayanai a karkashinsa dauke da sunan Muhuyin.

Yadda tsamin dangantaka ta kullu tsakanin Muhuyi da Ganduje

Rahotanni sun tabbatar da cewa tun gabanin wannan mataki na majalisa, wasu kafofin watsa labara sun bayyana cewa an fara samun takun-saka tsakanin Muhuyi Magaji da bangaren gwamnati.

Kafofin sun rawaito cewa an fara samun rashin jituwar ne a lokacin da Muhuyi ya yi yunkurin binciken iyalin gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan wasu kwangiloli da ake zargin sun saba ka’ida.

To sai dai gwamnatin ta musanta wannan zargin, haka kuma shi ma Muhuyi din bai ce komai kan zargin ba.

Sai dai wani bincike da BBC ta yi ta gano cewa akwai rashin jituwa sosai tsakanin Muhuyi Magaji da iyalin gwamnan Kano, wanda kuma ake gani shi ne babban dalilin da ya haifar da wannan tsamin dangantaka.

Gabanin shiga wannan yanayi dai, Muhuyi Magaji na daga cikin jami’an gwamnati mafiya tasiri a gwamnatin Abdullahi Ganduje, kuma gwamnan ya ba shi cikakkiyar damar yin aikinsa na yaki da cin hanci da rashawa, sannan ana yi masa kallon wani babban na hannun-daman gwamna.