Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta ta tabbatar da kame wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, a yankin Agbarho na Karamar Hukumar Ughelli da ke Jihar.
Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Onome Onovwakpoyeya ne ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya hakan a garin Warri a ranar Laraba.
- Rikicin Tibi da Jukun ya ritsa da rayukan ’yan sanda a Taraba
- An kashe Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda a Kuros Riba
- Tsohon Sarkin Kano ya magantu kan dakatarwar da aka yi wa Sheikh Abduljabbar
- An kama kani a cikin masu garkuwa da matar wansa a Zariya
“Da gaske ne rundunarmu ta cafke wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.
“Amma an maida su baban sashen binciken manyan laifuka da ke hedikwatar ’yan sanda,” cewar Onovwakpoyeya.
NAN ta rawaito cewa an cafke wanda ake zargin ne a ranar Talata a yankin Agbarho da ke jihar.
Bincike ya gano suna da hannu a garkuwar wani mutum mai suna Emmanuel Piopio, ranar Lahadin da ta gabata.
An kama masu laifin a dajin Ophori-Agbarho tare da hadin gwuiwar sojoji da ’yan banga.