✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun bindige ’yan bindigar Batsari

Rundunar ’Yan Sandan ta Jihar Katsina ta kashe ’yan ta’addan da ake zargi da kai hare-hare ne a Karamar Hukumar Batsari. Kakakin rundunar, SP Gambo…

Rundunar ’Yan Sandan ta Jihar Katsina ta kashe ’yan ta’addan da ake zargi da kai hare-hare ne a Karamar Hukumar Batsari.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isa, ya shaida wa ’yan jarida cewa rundunar ta samu nasarar ce bayan wani farmaki da mahara kusan 40 suka kai a kauyen Zamfarawa a karamar hukumar a ranar 6 ga watan Agusta.

Ya ce ’yan bindagar sun kashe kashe dattawa biyu da suka hada da Yakubu Idris mai shekaru 70 da kuma Shafi’u Suleiman mai shekaru 65, sannan suka yi awon gaba da dabbobi masu yawa.

Bayan samun rahoton harin ne ’yan sanda karkashin baturen yankin Batsari, suka bi sawun maharan da suka shige cikin jeji inda suka yi musayar wuta da su.

Ya ce ’yan sandan sun kashe mutun daya nan take yayin da saura da suka samu raunuka suka sha da kyadar a cikin dajin.

Har ila yau, ’yan sanda sun yi nasarar kwato shanu 30.

Washegari rundunar ta je kauyen Barankada bayan samun rahoto, inda ta tsinci gawarwakin mutun 7 daga cikin wadanda aka harba suka shiga daji da raunukan.

Ta ce ta kuma gano wasu layu da maharan ke amfani da kudi Naira dubu ashirin da ’yan kai da kuma alburusai da wasu kaya da aka tabbatar na maharan da aka kashe ne.