✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sanda sun bindige dan fashi a Katsina

’Yan Sanda a Jihar Katsina sun kashe wani dan fashi yayin wata arangama a kan babban titin Bakori zuwa Kabomo ranar Talata. Jami’an ’yan sandan…

’Yan Sanda a Jihar Katsina sun kashe wani dan fashi yayin wata arangama a kan babban titin Bakori zuwa Kabomo ranar Talata.

Jami’an ’yan sandan a yankin Bakori sun kai dauki ne a inda ’yan fashin suka tare hanya cikin dare sannan suka hallaka dan fashin.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya shaida wa manema labarai cewa “’da misalin karfe 8:30 na dare wasu ’yan fashi sun tare hanyar Bakori, amma mun farmake muka kashe daya daga cikinsu”.

Ya kara da cewa ragowar sun tsere yayin da aka samu bindiga kirar hannu a wajen wanda aka kashe din.

SP Gambo ya ce tuni rundunar ta fara bincike domin gano inda ragowar suka shiga.