Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta bayyana gawar wasu ’yan bindiga uku da suka addabi Karamar Hukumar Dutsinma ta Jihar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Sanusi Buba ne ya bayyana hakan yayin da ganawa da manema labarai a Hedikwatar ’yan sandan jihar, ranar Talata.
- Kai wa Fulani hari ba zai haifar wa da Najeriya da mai ido ba —Bashir Tofa
- Bata gari sun kone caji ofis sun sace makamai
- Za mu kawar da ayyukan ta’addanci a Katsina —Shugaban ’Yan Sanda
“Jami’anmu sun yi wa ’yan bindigar kwanton bauna yayin samamen da suka kai a tsakanin kauyen Mara da Tashar Gajere, da ke Karamar Hukumar Danmusa.
“Sun kuma yi nasarar kashe uku daga cikin ’yan bindigar tare da kwato bindigogu biyu kirar AK47, da harsasai 47.
“Ana ci gaba da binciken yankin don kame ragowar da suka ji rauni.
“Rundunar ’Yan Sandan Katsina na kara samun nasara a yaki da ’yan bindiga,” inji Buba.
Ya kara da cewa nasarar da jami’an tsaron suka samu ya biyo bayan kiran agaji da Kwamandan ’Yan Sandan Dutsinma, Aminu Umar ya samu cewa ’yan bindiga sama da 50 sun kai wa kauyen Unguwar Bera da kauyen Tashar Mangoro farmaki.