✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda na samun bayanai kan kisan Farfesa Falaki

Mataimakin Sufeto ‘Yan sanda mai kula da shiyya ta daya Alhaji Tambari Yabo Mohammed ya ce rundunar tana ci gaba a binciken da take yi…

Mataimakin Sufeto ‘Yan sanda mai kula da shiyya ta daya Alhaji Tambari Yabo Mohammed ya ce rundunar tana ci gaba a binciken da take yi kan kisan Farfesa Ahmad Mustapha Falaki Daraktan Cibiyar Nazarin Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Alhaji Tambari Yabo ya ce tuni rundunarsu ta samu nasarar cafke daya daga cikin mutum 11 da ake zargi da kashe Farfesan. “daya daga cikin mutum 11 da ake zargi da kashe Farfesan yana hannunmu. Sai dai ragowar sun gudu, kasancewar tunda aka yi kisan mutanen kauyen Fala suka tsere.”
A cewarsa rahoton da suka samu daga Asibitin Malam Aminu Kano ya nuna cewa Farfesan ya rasa ransa ne dalilin duka da ya sha ba wai harbi ba.
Game da bayanan da aka samu daga ’yan sandan Jihar Bauchi cewa sun kama mutum uku da ke da hannu a cikin kisan Farfesan, Tambari ya ce bincikensu ya saba da abin da ’yan sandan Bauchi suka bayyana. “Ban karyata cewa sun kama mutum uku, sai dai ba
gaskiya ba ne a ce wadanda suke zargin su ne suka kashe Farfesa Falaki ba. Ina ganin wadanda ake zargin sun fadi haka ne don cika baki da kuri kawai,” inji shi.
Ya tabbatar da cewa za a dauki matakin da ya dace kan lamarin, inda ya ce tuni aka fara yi wa ’yan sandan da aka yi kisan a gabansu tambayoyi. “Bai kamata a yi gaggawar yanke hukunci cewa ’yan sanda ne suka kashe Farfesan ba. Ina tabbatar wa jama’a cewa ba wanda zan goya wa baya, za mu yi kokarin ganin mun gurfanar da duk wadanda ke da
hannu a kisan gaban kuliya,” inji shi.
Idan za a iya tunawa Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi DSP Haruna Mohammed ta ce ta kama wani mai suna Lawan Ali dan asalin Jihar Borno da hannu a kisan Farfesan baya ga wasu mutum uku da ta kame tun farko da ake zargi da hannu a kisan.