Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano, ta mayar da martani da nuna jin daɗi ga ficewar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, zuwa Jam’iyyar APC kwanan nan, inda ta ce ficewarsa za ta kawo zaman lafiya a jam’iyyar.
Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan Sanata Kawu Sumaila ya bayyana ficewarsa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC.
- An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure
- Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Shugaban NNPP na Jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa, ya yi watsi da muhimmancin tafiyar da jam’iyyar tare da Kawu, inda ya bayyana shi a matsayin, “Wani mai taurin kai” wanda kasancewarsa a jam’iyyar ya fi kawo cikas fiye da amfani.
“Ba mu yi mamaki ba saboda wani abu ne da muka daɗe muna tsammani, dangane da batun jam’iyyarmu, mun riga mun dakatar da shi saboda ba shi da wata ƙima da zai ƙara, shi ya sa ya ci gaba da zama ba amfanin a cikinta,” in ji Dungurawa.
Dungurawa ya bayyana cewa, ficewar Kawu Sumaila ba asara ce ga Jam’iyyar NNPP ba, sai dai wani mataki ne da ya dace da zai dawo da kwanciyar hankali a cikin jam’iyyar.
“A yanzu jam’iyyar za ta samu zaman lafiya, ya kasance mai taurin kai a cikin ’yan jam’iyyar, don haka ficewar shi yana nufin jam’iyyar za ta iya mayar da hankali kan abin da ya kamata ta yi, saɓanin lokacin da yake nan yana hargitsa jam’iyyar,” in ji shi.