Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ba da sanarwar neman malamin addinin nan na Jihar Bauchi, Dokta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ruwa a jallo.
Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ’yan sandan Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakil bisa umarnin Kwamishinan ’yan sandan jihar.
- Gwamnatin Kano za ta fara kai samame rumbunan da aka ɓoye kayan abinci
- Kisan Nafi’u: Kotu ta sa a duba kwakwalwar Hafsat Chuchu
Sanarwar ta ce ana cigiyar malamin ne kamar yadda Babban Sufeton ’Yan sanda na Kasa, IGP Kayode Egbetokun ya ba da izini.
Sanarwar ta nemi duk wanda ya ga malamin to ya sanar da mahukunta mafi kusa, ko ya kama shi ya miƙa shi ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Haka kuma, sanarwar ta ce duk wanda ya ga malamin yana iya miƙa shi ofishin mataimakin kwamishinan ’yan sanda da ke kula da sashin binciken manyan laifuffuka na rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi ko a kira lambar waya kamar haka; 08151849417 ko 09048226246.
Tunda farko dai malamin ya dauki hankalin jama’a ne bayan wani furucin da ya yi da ake zargin ya munana ladabi ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) cewa ba ya neman taimakonsa sai na Allah.
Wannan kalamai da yayi ya jawo cece kuce har wassu malamai na ganin ya zagi Annabi , yayin da wassu ke gani maganane kan Tauhidi.
Ana dai tuhumar Dokta Idris ne da laifuka biyu da suka haɗa da kalaman batanci ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W, sai kuma laifin tayar da zaune tsaye.
Har yanzu dai ba a fara sauraron wannan shari’a ba kan waɗannan tuhume-tuhume.
Amma a baya ya yi zaman gidan kaso kan waɗannan tuhume-tuhume na tsawon kwana 39 tsakanin watan Yuni da Yuli, in ji lauyansa.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Mayun bara ne Kungiyar Fityanul Islam ce ta maka malamin a Kotun Majistare da ke Jihar Bauchi, bisa zargin sa da kalaman batannci ga Manzon Allah (SAW), zargin da malamin ya musanta.
A kwanakin baya ne wadansu kungiyoyin addini guda 17 karkashin kungiyar Fityanul Islam, ta rubuta takardar koke ga kwamishinan ’yan sandan jihar, bisa zargin Malamin ya yi batanci ga Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi).
Lamarin da ya sanya ke nan ’yan sanda gayyatar dukkan bangarorin da abin ya shafa inda Dokta Abdulaziz, wanda shi ne babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, ya amsa gayyatar ’yan sandan kafin daga bisani aka gurfanar da shi a gaban kotu kan wannan zargi.
Malamai da dama daga ciki da wajen Jihar Bauchi sun yi ta raddi kan yunkurin kama malamin, inda suke cewa ba daidai ba ne a ce za a kamashi a kan tauhidi, lamarin da ya jawo kwamishin ruwa na Jihar Bauchi Abdulrazaq Nuhu Zaki ya ce Gwamnatin Bauchi ba hannunta waje kama malamin.