Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa tana neman sanata Dino Melaye ruwa a jallo.
Sanarwar ta nuna cewa ana neman sanatan ne da dan tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Abubakar Audu mai suna Mohammed Audu.
Rundunar ta ‘yan sanda ta ce tana neman mutanen guda biyu bisa zargin ba ‘yan sanda labarin karya, inda Dino ya yi zargin cewa an kai masa hari da nufin kashe shi bara.