✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda biyu sun rasu, 17 sun jikkata a hatsarin mota a Filato 

Jami'an 'yan sanda mata biyu ne suka rasa rayukansu a hatsarin.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno ta sanar da mutuwar jami’anta biyu mata yayin da wasu 17 kuma suka jikkata a sanadiyar wani hatsarin mota da ya auku a Jihar Filato.

Hatsarin ya afku ne a ranar Litinin a kan hanyar Hawan Kibo a Jihar Filato, yayin da ‘yan sandan da abun ya shafa ke kan hanyar zuwa Uyo domin gudanar da gasar wasannin ‘yan sanda na shekarar 2022.

Kakakin rundunar, Sani Shatambaya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarawa da ya fitar ranar Talata a Maiduguri.

Ya ce tawagar za ta wakilci shiyya ta 15 da ta kunshi Jihohin Borno da Yobe a gasar wasannin ‘yan sanda da za a Uyo, a Jihar Akwa Ibom.

Kakakin ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon shanyewar birki, inda ya kara da cewa wadanda suka mutu ‘yan sanda guda biyu ne mata.

“Kwamishanan ‘yan sandan Jihar Borno wanda ya yi alhinin afkuwar hatsarin ya ce an dawo da jami’an da suka rasa rayukansu da wadanda suka jikkata zuwa Maiduguri,” in ji shi.

A cewar Shatambaya, an gudanar da jana’izar ga wadanda suka mutu, yayin da wadanda suka jikkata ke samun kulawa a asibitoci daban-daban a Maiduguri.

“Kwamishanan ‘yan sandan wanda ya jagoranci tawagar rundunar a Borno, ya jajanta wa iyalan jami’an da suka rasu.

“Ya kuma yi addu’a ga sauran ‘yan sandan da suka ji rauni fatan samun lafiya,” in ji shi.