Gwamna Dikko Radda na Katsina ya sake koka cewa ’yan sanda 32 ne kawai ke sintiri a ƙaramar hukuma daya a jihar.
A hirarsa da DW Hausa, gwamnan ya ce bindigogi tara aka ba wa ’yan sandan, kuma a halin yanzu biyar daga cikin bindigogin ne suke aiki.
Ya ce: “A yanzu haka a Jihar Katsina akwai karamar hukuma mai ’yan sanda 39 da bindigogi guda tara, waɗanda biyar daga bindigogin ne suke aiki,” in ji Dikko Radda.
Duk da cewa bai ambaci suna ba, amma ya ce, “Karmar Hukumar tana da gundumomin siyasa 10, tare da kauyuka sama da 200.
- ’Yan takarar ciyaman 20 a Kano ’yan ƙwaya ne —NDLEA
- Ambaliya ta kashe ’yan Boko Haram a Dajin Sambisa
- Ambaliyar Maiduguri: Ruwa ya tono gawarwaki, mutane 200,000 sun rasa gidajensu
“Ta yaya rundunar ’yan sanda da ma’aikata 39 za ta iya kare su?
“Mun bullo da wani shiri wanda duk wata al’umma da ke shirye ta kare kanta, za mu ba su goyon baya da horon da ya dace don fuskantar ’yan ta’adda kafin zuwan jami’an tsaro.”
Jihar Katsina ta jima tana fama da munanan hare-haren ’yan bindiga.
Kwanakin baya Gwamna Dikko Radda ya yi kira ga al’ummar jihar da su ɗauki matakan kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga.
Ya yi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi a Daura.
A cikin wani bidiyo, Radda cikin fushi ya bukaci malaman addinin Musulunci da su faɗakar da jama’a kam muhimmancin kare kai kamar yadda addinin ya tanada.
Gwamnan yayi irin wannan kiran a watan, sannan kwamishinansa na tsaro, Nasiru Muazu Danmusa, ya yi irin wannan roko a kwanan baya.