Asirin wasu dalibai biyu ’yan sakandare ya tonu a lokacin da suka yi garkuwa da kansu tare da neman kudin fansa daga hannun iyayensu.
Rundunar tsaro ta Amotekun a Jihar Ondo ce ta kama daliban a wani otal da suka boye kansu a garin Oka-Akoko cikin Karamar Hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma.
- Yanayin kasuwa ne ya sa man fetur ya kara tashi — NNPC
- Kungiyar kwadago ta yi watsi da sabon karin farashin man fetur
Da yake yi wa ’yan jarida karin haske a ofishinsa da ke Akure, babban birnin Jihar, Kwamandan tundunar ta Amotekun wanda kuma shi ne mai ba Gwamnan Jihar shawara a kan tsaro, Akogun Adetunji Adeleye, ya ce an yi nasarar kama daliban ne ta hanyar bin sahun lambar wayar da suka kirawo iyayen nasu suka sauya murya.
Ya ce daliban dai sun nemi a biya su kudin fansa Naira dubu 100 cikin awoyi 2 ko su hallaka wadanda suka tsare.
“Bayan samun wannan labari daga iyayen wadannan dalibai ne muka hanzarta daukar matakin gano maboyarsu a wani otal a garin Oka-Akoko inda muka same su sanye da rigunan makaranta suna jiran a kawo masu kudin fansa,” in ji Kwamandan.
Daya daga cikin daliban ta ce ta yanke shawarar yin garkuwa da kanta ne a dalilin tursasawar da mahaifiyarta take yi mata a kowane lokaci.
Ta ce ta hada baki da ’yar uwarta ne da suka kulla cewa za tayi amfani da kudin fansar ne wajen hukunta mahaifiyar da ta hana ta sakat.
Kwamanda Adetunji Adeleye ya ce daliban da aka kama da bai bayyana sunayensu ba masu shekaru 13 da 15, ’yan makarantar Sakandare (JSS 3) da (SSS1) ne da aka nuna su ga ‘yan jarida tare da wasu mutane 26 da ake zargi da aikata miyagun ayyuka a sassa daban daban na Jihar Ondo.