✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan sa-kai sun yi wa shugaban Fulani yankan rago a masallaci

Sun fito da shi yayin da ya ke jan sallah a masallaci.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina ta tabbatar da kisan gillar da wasu ’yan sa-kai suka yi wa Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah na Karamar Hukumar Bakori a jihar, yayin da yake limancin sallah a cikin masallaci.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin ’yan sandan jihar, Gambo Isah, ya ce hakan ya sanya ’yan bindiga suka kai harin daukar fansa yankin inda suka kashe mutane da dama.

A cewarsa, “Ayyukan haramtattun ’yan sa-kai a wasu yankuna na jihar nan ya kara ta’azzara lamura, wanda a dalilin haka Fulani da dama da ba su ji, ba su gani ba, suka rasa rayukansu, ciki har da Shugaban Miyetti Allah na Karamar Hukumar Bakori wanda suka yi wa yankan rago, hakan ya sa ’yan bindiga kai harin daukar fansa.”

Ya kara da cewa harin da ’yan bindigar suka kai a yankin Daudawa da Yasore na daga cikin hare-haren daukar fansa da suka kai a jiharsa.

Gambo Isah ya kara da cewa in har shugabanin yankunan suka ci gaba da yin shiru ko goyon bayan ayyukan ’yan sa-kai, samun zaman lafiya zai yi wuya a jihar.

Ya jadadda cewa dole ne kowa ya fito ya yi Allah wadai da ayyukan na ’yan sa-kai da kisan mutanen da babu ruwansu.

Kakakin ya kara da cewa ’yan sa-kan na ci gaba da kashe Fulani suna musu fashi dukiyoyinsu, ciki har da amfanin gona da suka girbe.

Amma ya kara tabbatar wa jama’ar jihar cewa an haramta ayyukan ’yan sa-kai a jihar, inda ya ce ayyukan ta’addanci ba iya kan ’yan bindiga ya tsaya ba, har da ’yan sa-kai.