’Yan sintirin da aka haramta a Jihar Katsina wadanda aka fi sani da ’Yan Sa Kai sun kashe Fulani makiyaya 14 a Karamar Hukumar Kurfi ta jihar a ranar Litinin.
Mazauna yankin sun ce ana zargin wadanda aka kashe din ’yan bindiga ne da suka hana jama’ar yankunan sakat.
- ”Yan sa kai na neman cin karensu ba babbaka a Kebbi’
- ‘Yan bindiga sun kashe limami da mutum 9 a Katsina
“Yawancin wadanda aka kashe din na zaune ne cikin rugagensu kusa da kauyen Wurma na Karamar Hukumar Kurfi, kuma sun jima suna cin karensu ba babbaka a yankin”, inji wani mazaunin yankin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, Gambo Isa ya ce ’yan sa kan sun yi wa makiyayan yankan rago ne, abin da ya yi tir da kuma ya ce ba za a lamunta ba.
Ya ce, “Mun riga mun fara bincike da nufin ganin mun kamo masu laifin domin su girbi abin da suka shuka.
“Babu wata al’umma da ta san abin da take yi da za ta zuba ido irin hakan na faruwa, wanda hakan ne ma ya sa Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta aikin sa kan tun da farko”, inji shi.