✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan janye sunan Maryam Shetty daga jerin ministoci

Cin fuska ne, kuma ba za ta taɓa warkewa daga wannan ƙaskancin da aka yi mata ba.

Ana tsaka da fara tantance minitoci rukuni na biyu da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika majalisa, aka samu labarin cewa ya sauya sunan Maryam Shetty da na Mariya Mahmoud a matsayin minista daga Kano.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ne ya sanar da wannan sauyin a zauren Majalisar.

A ranar Laraba ne dai shugaba Tinubu ya bai aike wa Majalisar sunan Maryam Shetty a matsayin ɗaya daga cikin ministocin da zai naɗa daga Kano.

Sai dai cire sunan nata ya jawo cece-kuce musamman a soshiyal midiya kasancewar abin ya zamo ba-zata.

Me ’yan Najeriya ke cewa?

Jin kadam bayan samun wannan labari masu amfani da shafukan sada zumunta suka yi ca akan batun cire sunan nata, inda da dama ke bayyana ɓacin ran su game da abin da wasu ke ganin cin fuska ne.

Matasa ‘yan gwagwarmaya mata da maza suna ta tsokaci kan batun da suke ganin akwai lauje cikin nadi.

Zainab Naseer Ahmad, cewa ta yi “Na kasa cewa komai, ina miki addu’a da fatan alheri Maryam Shetty, amma gaskiya wannan abin baƙin ciki ne.”

Sani Isah Obajana ya ce “Maganar gaskiya ban ji daɗi na cire sunan Maryam ba, saboda mun gaji da ganin tsofaffin gwamnoni a tafiya irin wannan”

Uncle Anass Dukura cewa yake “Kai in ban da ma dai lamarin hassada wawan abu ne, ta yaya ba ka yi bakin cikin sanya wanda baka san shi ba, ba ka san wanda ya san shi ba, amma ka zo ka kasa barci akan an sanya wanda ko baka san shi ba, ka san wanda ya san shi? Mtschew.”

Shi ma wani matashin dan siyasa, Adnan Muktar TudunWada da ya yi tsokaci cikin harshen Turanci ya ce “Labari ne mara daɗi ga matasa, amma Allah Ya fi sanin daidai, Allah Ya sa haka shi ne mafi alkhairi.”

Shi ma ɗan Jarida Jaafar Jaafar ya ce “Tulumbu bai kyauta mana ba”. Abdulaziz T Bako ya ce “Wani karin tabbaci cewa wannan gwamnatin ita ma birkitacciyar ce. Allah ya kyauta!”.

Yusuf Ibrahim Kudan ma ya ce “Gaskiya Banji dadin Cire sunan Wannan matashiya ba Kuma hakan ya nuna Matasa Basu da baki kenan a wannan gwamnatin”.

Shi kuma Karibullah Ahmad Namadobi ya ce “Na jima ban ji labarin da ya bata min rai ba irin wannan. Allah Ya raba mu da sharrin masu sharri. Wadannan tsafaffin ’yan siyasar kullum burinsu dakile matasa, in dai ba ƴaƴan cikinsu ba ne.

Hassada ce ta jawo hakan…

Sai dai a gefe guda wasu na ganin surutan da aka yi ta yi ne bayan naɗin nata, yayin da wasu ke cewa siyasa ce ta shiga cikin lamarin

Wani mai amfani da shafukan sada zumunta Tahir Ibrahim Tahir cewa ya yi “Kun ga illar harshenmu da rubutun mu a social media ko? Lallai idan haka za mu ci gaba da yiwa ’yan uwanmu matasa to a haka zamu ƙare kullum wajen yi musu kirari su da”

Aliyu Samba ya ce “Da yawa mutane karya suke a fadinsu na cewa a dinga bai wa matasa dama. Duk lalacewar uban gidan su yafi dan uwan su matashi duk cancantar sa”.

Abba D Imam Tofa kuwa a ganin sa in da matasan Kudancin Najeriya ba za su yi hakan ba, domin a cewar sa “Matasan Kudu da yake akwai technicality da aka ba DR Betta Edu, Solidarity kurum suke mata!.

A cewar Aliyu Dahiru Aliyu “Ko ba komai duk wanda ya san Maryam Shetty ya san mutuniyar kirki ce.

“Ko mu da muke jam’iyyar adawa tana mutuntamu cikin nishadi da dariya. Ni ko sunana ba ta fada sai dai ta ce “kanina”.

“Amma ’yan bakin ciki kuka dinga surutu karshe sai da suka samu damar canja ta da matar da a shekara hudunta tana kwamishiniya a karkashinta ba abin da aka yi sai rufe makarantu da gine gefunansu.

“A lokacin ilimi ya yi lalacewar da bai taba yi ba a tarihin Jihar Kano. Yanzu sai ku ji dadi tun da ku matasa ku ne makiyan kanku.”

Wani mai amfani da shafin Facebook, Yusuf Muhammad Gidan Dare cewa ya yi “Baya ta haihu, matasa ko mahassada” yayin da Hassana Magaji ta ce “Wallahi Arewa mu ne matsalar kan mu”. Shi kuma Abbas Salihu Ahmad ya ce “Allah dai Ya san gobe”.

Ra’ayin Badamasi Bello Dinawa cewa yake “Kai ka san ana minahicci da rainin wayo a ƙasar nan! The same mutanen da su ka rinƙa shaguɓe lokacin da aka bayyana sunan Dr. Shetty, su ne kuma yanzu su ke cewa ba a kyauta ma ta ba.”

Sherrif Almuhajir ya bayyana alhinin sa, inda ya ce “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibati. Shikenan ’yan bakin ciki kowa ya huta. My sister, Allah Ya zaba miki ma fi alheri.

An maye sunan Shetty da na Dr Mariya Mahmoud kwamishina a gwamnatin Ganduje da ku tsohon Minista a gwamnatin Buhari Festus Keyamo
An maye sunan Shetty da na Dr Mariya Mahmoud kwamishina a gwamnatin Ganduje da kuma tsohon Minista a gwamnatin Buhari Festus Keyamo

Abin da ‘yan Tuwita ke cewa…

A leken da Aminiya ta yi a shafin Tuwita, an ambaci sunan Maryam Shetty kusan sau dubu 30.

Yawancin su suna bayyana bacin rai da kuma damuwa akan yadda matasa za su iya samun dama a irin wannan lokaci idan har za a ci gaba da tafiya a haka.

NAJERIYA A YAU: Makomar Jam’iyyar APC Bayan Zaɓen Ganduje

Peacock @dawisu da ya bayyana ra’ayin sa a harshen turanci, cewa yayi “Na tausaya wa Maryam Shetty, ko da a ce tana da ƙwarewar ta zama minista ko a’a. Abin ɓacin ran shi ne, tsarin da aka bi wajen miƙa sunanta da kuma yadda aka janye, wannan cin fuska ne, kuma ba za ta taɓa warkewa daga wannan ƙaskancin da aka yi mata ba.”

Sarki @Waspapping_ cewa yayi “Ban san wace ce Maryam Shetty, ko kuma abin da za ta iya yi ba, amma wallahi ina da yaƙinin za ta taka muhimmiyar rawa a matsayin minista fiye da waɗanda ba su da cancanta.”

Shi ma Akin Akinwale @mrlurvy ya ce “Cire sunan Maryam Shetty na ɗaya daga cikin abin da ya fi karya zuciya a siyasance bayan na David Lyon”.

Me Maryam Shetty ta ce?

Tun da farko an yaɗa wani takaitaccen bidiyo da ke nuna Shetty ɗin ta isa majalisa domin tantance ta, amma ta samu labarin cewa an sauya sunan nata.

Sai dai har yanzu Maryam Shetty ba ta ce uffan kan batun ba, duk da yake an yi ta yada wasu bayanai a shafukan Tuwita da da cewar ta samu labarin hakan, har ma aka ruwaito shafin na taya murna ga sabuwar matar da aka miƙa sunan ta.

Bayanan da Aminiya ta samu sun tabbatar da cewa Shetty ɗin ba ta da wani shafi a Tuwita.

Tuni wasu ke ta fatan alkhairi da bukatar a saka mata da wani muƙamin da zai zama a madadin wannan.

Kawo yanzu mutum 48 ne Tinubu ya mika wa majalisar domin tantancewa, inda a ranar Laraba ta kammala tantance mutum 28 na farko.

Da haka, Tinubu zai zama shugaban kasa da ministocinsa suka fi yawa a Najeriya a Jamhuriya ta hudu. Kafin yanzu, magabancinsa, Muhammadu Buhari, ne ya fi yawan ministoci, inda yake da 43.