✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Minista: Tinubu ya maye Maryam Shetty da Mariya Mahmoud

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Maryam Shetty da na Mariya Mahmoud a matsayin minista daga Kano. Da safiyar Juma’a ne shugaban Majalisar…

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauya sunan Maryam Shetty da na Mariya Mahmoud a matsayin minista daga Kano.

Da safiyar Juma’a ne shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio ya sanar da wannan sauyin a zauren Majalisar.

A ranar Laraba ne dai shugaba Tinubu ya bai aike wa Majalisar sunan Maryam Shetty a matsayin ɗaya daga cikin ministocin da zai naɗa daga Kano.

Sai dai naɗinta ya jawo cece-kuce musamman a soshiyal midiya kasancewar abin ya zamo ba-zata.

Wacece Mariya Mahmoud?

Dr Mariya Mahmoud ita ce kwamishinar ilimi mai zurfi a zamanin gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Kafin zama kwamishina kuma likita ce a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.