✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ganduje ya zama silar janye sunan Maryam Shetty daga jerin ministoci

Dakta Maryam Shetty ta ce kaddara ce ta sa a ka cire sunanta.

A yayin da ’yan Najeriya ke ci gaba da yamutsa hazo kan batun nadin Maryam Shetty a matsayin daya daga cikin ministocin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma janye sunanta sa’o’i kalilan gabanin tantance ta, binciken Jaridar Daily Trust ya gano inda gizo yake saka.

Maryam Shetty dai ta kasance matar da sunanta ya rika gudana a kan harsunan jama’a a ciki da wajen Najeriya tun bayan da Shugaba Tinubu ya mika sunanta a cikin rukuni na biyu na jerin ministocin da zai nada.

Sai dai Shugaba Tinubu ya kai jama’a ya baro, inda a ranar Juma’a ya aike wa da Majalisar Dattawa sakon janye sunanta tare maye gurbinsa da na wata mai suna Dokta Mariya Mahmoud Bunkure.

Dokta Mariya Bunkure tsohuwar Kwamishinar Manyan Makarantu ce ta Jihar Kano a zamanin Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje.

Yadda Ganduje ya zama sila

A binciken da Daily Trust ta gudanar, tunda farko dai wani babban jami’i a Fadar Shugaban Kasa ne ya cusa sunan Maryam Shetty cikin jerin sunayen ministocin na Tinubu, yayin da fadar ta yi zaton cewa, da sanin Ganduje aka bayar da sunan nata daga jihar Kano.

Sai dai wasu makusantan tsohon Gwamnan na Kano sun shaida wa Daily Trust cewa, babban dalilin da ya sa Ganduje ya nuna karfin iko har aka sauya Maryam da Bunkure shi ne cewa, ba ta cikin mukarraban siyasarsa a lokacin da yake gwamnan, sannan ta yi kaurin suna wajen sukar manufofinsa a lokacin da yake gwamna.

Bugu da kari, Shetty na da kusanci sosai da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi, inda har ta yi ta caccakar gwamnatin Ganduje kan yadda ta sauke Sarkin daga karagar mulki, abin da wasu majiyoyi suka bayyana a matsayin daya daga cikin dalilan janye sunanta.

Wakilinmu ya rawaito cewa, shugaba Tinubu ya yi matukar mamaki bayan ya samu labarin cewa, ba Ganduje ba ne ya gabatar da sunan Maryam Shetty, inda mutanen da suka zabe ta suka nuna wa shugaban wani hoto da ta dauka da Gandujen don nuna cewa, tana tare da shi.

Dalilin da Mariya Bunkure ta samu shiga

Mariya Mahmoud Bunkure ita ce Kwamishinar Ilimi Mai Zurfi a zamanin gwamnatin Ganduje, sai dai ba ta cikin sahun farko na wadanda aka yi tsammanin za su samu gurbi a jerin ministocin da Tinubu zai nada.

Sai dai kuma ta samu shiga inda ta yi wa sa’o’inta fintikau kasancewar Tinubu ya jaddada cewa dole wacce za ta maye gurbin Maryam Shetty daga Jihar Kano ta kasance mace, la’akari da aniyarsa ta bai wa mata wani kaso a Majalisar Zartarwa.

A cewar makusantan Ganduje, “Dokta Mariya tana da shiga sosai a wurin iyalan tsohon gwamnan, a yayin da duk sauran wanda aka yi shirin tura sunayensu sun kasance maza, saboda haka ne Oga [Ganduje] ya ba da sunanta.

Kafin zaman Dokta Mariya kwamishina  a gwamnatin Ganduje, ta kasance likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano.

Haka kuma, Dokta Mariya da Maryam Shetty kawaye ne inda suka yi aji daya tare a karamar sakandire. Sannan kuma suka sake haduwa yayin da karatu ya kai su Jami’ar Bayero da ke Kano, inda Mariya ta yi karatun likitanci yayin da Maryam ta yi nata a fannin kula da lafiyar masu jinya.

A yayin da Maryam Shetty ta shahara wajen gwagwarmaya musamman a dandalan sada zumunta, ita kuwa Dokta Bunkure ta yi nata sunan ne bayan da Ganduje ya nada ta Kwamishina a wa’adin mulkinsa na biyu.

Haka kuma, bayanai sun ce Dokta Mariya kawa ce ga Amina Ganduje, daya daga cikin ’ya’yan tsohon gwamnan wadda kuma ta yi silar nada ta mukamin kwamishina.

Martanin Maryam Shetty

Tuni Shetty ta rungumi wannan sauyin da hannu biyu-biyu, tana mai cewa, haka Allah Ya tsara, yayin da kuma ta yi wa gwamnatin Tinubu fatan alheri gami da jinjina.

Dakta Maryam Shetty ta ce kaddara ce ta sa a ka cire sunanta.

Cikin wani dogon sako da ta wallafa a shafinta na Facebook Maryam Shetty, ta ce ba za ta iya bayyana irin farin cikin da ta ji ba a lokacin da ta ga sunanta cikin jerin mutanen da ake son nadawa a matsayin ministoci.

Kuma hakan a cewarta wata alama ce da ke nuna cewa a shirye Najeriya take wajen tabbatar da kyakkyawar makomar mata musamman matasa kamarta.

To sai dai Dakta Shetty ta ce kaddara wadda ta riga fata, ta yi tasiri wajen cire sunanta daga jerin sunayen.

Ta ce “wasu na ganin hakan tamkar wani koma-baya ne a gare ni, amma ni a matsayina na musulma na yadda da kaddara, na dauki hakan a matsayin kaddara daga Allah, wanda Shi Ke bayar da mulki ga wanda Ya so, kuma a lokacin da Ya so.”

Ta kuma kara da cewa duk, da wannan abin da ya faru, tana mika godiyarta ga Shugaba Tinubu kan sanya sunanta da ya yi tun da farko.

Dakta Maryam ta kuma ce hakan bai karya mata gwiwa ba, domin kuwa a cewarta tana cike da kwarin gwiwar bauta wa kasarta.

“Ina son tabbatar wa magoya baya na cewa wannan ba shi ne karshe ba, yanzu ma aka fara, don haka ku ci gaba da yi wa kasarmu addu’a tare da goya wa shugaban kasarmu baya.”