Majalisar Dattawa ta tantance Dokta Mariya Mairiga Mahmoud Bunkure a matsayin minista daga Jihar Kano.
Dokta Mariya dai ita ce wadda ta maye gurbin Maryam Shetty da Shugaba Bola Tinubu ya cire sunanta a satin daya gabata.
- Matan Kano da aka taba canza sunayensu a jerin ministoci
- An sace Sarki da matarsa a cikin fada a Nasarawa
Sauyan sunan Maryam Shetty da na Dokta Mariya Mairiga ya janyo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya.
A karshen makon da ya gabata ne tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje cikin wani bidiyo ya bayyana dalilin maye gurbin Maryam Shetty.
Sai dai wasu da dama daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta sun tofa albarkacin bakinsu.
Wasu na ganin rashin kyautawa na cire sunan matashiyar wadda ’yan uwa da abokan arziki suka rika taya ta murna bayan fitowar sunanta a cikin jerin wadanda Shugaba Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa domin tantancewa.
Sai dai Ganduje, a cikin bidiyon ya bayyana cewar mutanen Kano da kuma soshiyal midiya ce suka taka rawar gani wajen cire sunan matashiyar.
Daga cikin wadanda suka rabauta da kujerar minista a Kano, akwai sunan tsohon mataimakin gwamnan Kano, Abdullahi Tijjani Gwarzo karkashin tsohon gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau.