… Aikin sanya wayoyi mai nisan kilomita 120,000 yana tafiya
Shugaban Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC), Farfesa Umar Garba Dambatta ya ce jimillar ’yan Najeriya miliyan 70 ne suke amfani da Intanet.
Farfesa Garba Dambatta ya bayyana haka ne a ranar Lahadin da ta gabata a wajen taron mako na 39 kan fasahar sadarwa na GITED da ya gudana a Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.
Ya ce Najeriya ta samu nasarar cimma kashi 35 cikin 100 na samar da Intanet kuma za ta ci gaba har ya kai kashi 37a karshen bana. Ya ce kimanin aikin sanya wayoyi mai nisan kilomita dubu 120, a sassan kasar nan na ci gaba, kuma zai ci gaba da zagaya kasar don samar da Intanet mai karfin gaske.
“An ba kamfanonin da za su samar da tsarin (Infrascos) lasisin aiki, a kowane bangaren kasar nan,” inji shi. Ya ce, akwai alaka a tsakanin samun Intanet da samar da dukiya inda dimbin matasan Najeriya suke dada gogewa wajen bullo da sababbi da ingantattun dabaru da doka ta amince sakamakon samun hanyoyin Intanet.
Ya ce ba za a bar Najeriya a baya ba a shirin juyin masana’antu na hudu domin ta shirya wa hakan..