Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta ce kimanin mutum miliyan 25.3 ne za su fuskanci karancin abinci a fadin Najeriya a 2023.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, inda ta yi gargadin idan ba a dauki matakin dakile lamarin ba, mutum miliyan 4.4 za su fuskanci matsalar a jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
- Buhari Ne Ya Gina Hanyar Garinku, Ya Kori Boko Haram —APC Ga Atiku
- A kori duk jami’in gidan yari da bai iya harbin kisa ba —Minista
Hukumar, a cikin binciken abinci mai gina jiki na watan Oktoba na shekarar 2022 da ta yi, ta ce kusan mutum miliyan 17 ne a kasar ke tsaka da fuskantar matsalar karancin abincin.
Rahoton ya ce mutanen sun hada da ‘yan gudun hijira da wadanda suka fito daga jihohi 26, ciki har da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Bugu da kari, rahoton ya kuma ce mutum miliyan uku daga cikin wannan adadi na zaune ne a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe.
A wani yunkuri na taimaka wa wadanda lamarin ya shafa, gwamnatin kasar Norway ta sabunta hadin gwiwar samar da kudade da hukumar (FAO).
Wadannan kudade dai an samar da su ne da nufin taimaka wa al’ummar da ke fama da rauni a Jihohin Borno da Adamawa da Yobe da kuma Taraba.
Tsawon shekara uku za a yi ana amfani da kudaden, wadanda ake sa ran mutane da dama za su amfana, kuma akalla kaso 45 cikin 100 cikinsu mata ne.
Jakadan Norway a Najeriya, Knut Eiliv Lein, ya ce kasarsa na ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa kokarin da ake yi na maido da rayuwar mutanen da tashe-tashen hankula ya shafa a Arewa Maso Gabashin Najeriya.
“Wannan rattaba hannu da aka yi a yau wani bangare ne na tallafin da Norway ke bai wa Najeriya, ciki har da ayyukan jinkai musamman ga wadanda suke da bukata a yankin Arewa Maso Gabas,” inji Mista Lein.
“Mun yi hadin gwiwa da kungiyoyi wajen magance batutuwa da dama da suka hada da kiwon lafiya, samar da abinci, Dimokuradiyya, daidaiton jinsi da sauransu.”