Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ’yan Najeriya kukan dadi suke yi – domin kuwa da sun san irin halin matsi da takwarorinsu na kasashen Afirka ke ciki – da sun yi wa Allah godiya.
Buharin ya fadi haka ne yayin da ya kai wa Sarkin Katsina, Dokta Abdulmumini Kabir Usman ziyara fadarsa a ranar Asabar.
A cewarsa, zai ci gaba da yin bakin kokarinsa wajen inganta jin dadin al’ummar bayan ya saurari korafe-korafe kan halin da suke ciki daga wurin gwamna Aminu Bello Masari da kuma Sarkin Katsina.
“Da mutanenmu sun san irin halin matsin rayuwa da wasu kasashen Afirka ke ciki a halin yanzu, da sun gode wa Allah game da halin da suke ciki a kasar nan.
“Saboda haka muna kira ga mutane da su yawaita hakuri, muna iya bakin kokarinmu.
“Babu abin da ya fi zaman lafiya, muna rokon Allah Ya ba mu damar ganin bayan masu kokarin wargaza mana zaman lafiyar kasarmu,” a cewar Buhari.
Aminiya ta ruwaito cewa, bayan ziyarar da Buharin ya kai Fadar Sarkin Katsinan ce, kai tsaye ya koma Fadar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja bayan ya yi hutun Babbar Sallah a garin Daura.