✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya ku fito ku yi zaben gwamnoni – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga al’ummar Najeriya su…

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya yi kira ga al’ummar Najeriya su fito su zabi gwamnonin da za su taimaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zaben da za a gudanar gobe Asabar. Sheikh Sani Yahya Jingir ya yi kiran ne a lokacin da yake zanta wa da jaridar Aminiya a garin Jos.

Ya ce bai kamata ’yan Najeriya su yi kasa a gwiwa a  zaben gwamnonin ba.

“Don haka muna kira ga ’yan Najeriya su fito su zaba wa Shugaban Kasa gwamnoni nagari da za su taimaka masa,” inji shi.

Sheikh Jingir ya yaba da yadda aka gudanar da zaben Shugaban Kasa da ya gabata. Ya  ce Allah Ya taimaki Najeriya kan yadda aka gudanar da wannan zabe domin   ci gaban kasar da samar ilimi da zaman lafiya.

Sannan ya kira ga Shugaba Buhari ya dauki mutanen kirki da za su taimaka masa, kada ya dauki kara da kiyashi da za su kawo tarnaki irin wadanda suka gabata.

Sheikh Jingir ya kara da cewa bai kamata tsohon Mataimakin Shugaban  Kasa Atiku Abubakar da Shugaba Buhari su shiga kotu kan wannan zabe da aka gudanar ba. Domin dukansu kowa ya ce yana yin wannan takara ce domin ya  taimaka wajen gina Najeriya.

“Don haka a ganina bai kamata su shiga rigingimun shari’a ba. Su hada hannu wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya da ilimi da tsaro kamar yadda kowa ya yi alkawari. Domin dukkansu sun cewa Allah ne Yake bayar da mulki. Don haka su hada kai su bai wa marada kunya,” inji shi.