Wasu ’yan bindiga masu satar mutane sun kai hari unguwar Dawaki da ke Abuja, in da suka yi awon gaba da mutane 20.
Shugaban unguwar, Tunde Abdulrahim, ya ce ’yan bindigar da adadinsu ya kai 50, dauke da muggan makamai sun shiga rukunin gidaje na Dawaki Rock Heaven ne kafin Sallar Isha’i na yammacin ranar Lahadi.
Harin ya tashi hankalin jama’ar yankin, lura da cewa ’yan bindigar sun shiga gidaje har guda shida suna daukar mutane.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce jami’ansu karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda CP Benneth Igweh sun yi nasarar ceto duk wadanda aka sace.
- NAJERIYA A YAU: Tasirin Auna Hauhawar Farashi A Rayuwar Talaka
- Kotu ta tura wanda ya kona masallata a Kano zuwa gidan yari
Ta ce, “Mun samu kiran gaggawa daga unguwar Dawaki da misalin karfe 11:30 na daren ranar Lahadi, nan take Kwamishina, CP Benneth Igweh ya jagoranci runduna domin fuskantar ’yan bindigar”.
Josephine ta ce Kwamishinan da jami’ansa sun yi wa ’yan bindigar kofar rago a Ushafa da ke yankin Bwari, inda suka yi nasarar ceto mutanen da aka sace.
Kawo yanzu dai akwai mutum guda a asibiti yana karbar magani sakamakon rauni da ya samu sanadiyyar harbin bindiga.