’Yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu yara uku a Jihar Kaduna na neman kudin fansa Naira miliyan 30.
A makon jiya ne ’yan bindiga suka kutsa gidan wani likita suka yi awon gaba da ’ya’yansa uku a unguwar Azala da ke yankin Katari a Karamar Hukumar Kachia.
Wani makusancin iyalan likitan mai suna Barnabas, ya ce, “Iyalan sun shiga tashin hankali saboda rashin samun tuntuba daga masu garkuwar.
“Sai a ranar Asabar da misalin 11 na dare shugaban masu garkuwar ya kira yana neman kudin fansa Naira miliyan 30 da kayan abinci da kwaya kafin su sako yaran.”
A cewarsa, iyalan sun roki a sassauta kudin zuwa abin da za su iya.
Kawo yanzu kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna, SP Hassan Mansur, bai yi tsokaci kan lamarin ba.