Hukumar Karbar Korafi da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano ta yi wa Babban Asibitin Gwarzo tarar Naira dubu 500 kan bayar da bayanan karya game da ayyukan da ya gudanar.
Hukumar ta yi wa asibitin tarar ne bayan takardar neman biyan kudaden ayyukan da asibitin ya yi ikirarin gudanarwa, alhali kuwa ba a yi ayyukan ba.
An gano haka ne bayan binciken da sashen yaki da rashawa na hukumar lafiya ta jihar ya gudanar.
Yayin gabatar da rahoton, shugabar hukumar, Dokta Rahila Aliyu Mukhtar, ta ce a lokacin wata ziyara da aka kai asibitin ne aka gano tufka da warwara a bayanan kudaden aikin da hukumar asibitin ke neman gwamnati ta biya.
A sakamakon haka ne aka zurfafa bincike da aka gano karairayin, lamarin da ya sa aka yi musu tara.