Hukumomin Saudiyya sun ba Najeriya adadin kujera dubu 43 don sauke farali a shekarar 2022 da muke ciki.
Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Muhammad Abba Dambatta ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai a ranar Laraba.
- ’Yan Boko Haram sun kashe kwamandojin ISWAP 2 da mayaka 32
- Jiragen soji sun tarwatsa maboyar ’yan ta’adda a Taraba
Dambatta ya ce wannan ya biyo bayan yadda kasar ta Saudiyya ta ce mutum miliyan daya ne kawai za su gudanar da aikin Hajjin bana a fadin duniya.
Ya ce wannan adadi da aka bai wa Najeria na da alaka da yawan mutanen da Najeria take da su.
Muhammad Dambatta ya ce kodayake har yanzu Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ba ta fitar da kudin aikin Hajjin bana ba, amma alamu na nuna kudin zai karu.
Ya ce a baya ana canja Dalar Amurka a kan Naira 350 yanzu kuma ta kai Naira 408 da ke nuna lallai za a samu karin kudin.
A karshe ya ce a yanzu dai ana jiran hukumar ta bai wa kowace jiha adadin kujerunta tare da bayyana adadin kudin na bana.