✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya 264 sun kashe kansu a shekara hudu

Najeriya ce ta 30 a cikin kasashen duniya 183 inda mutane suka fi kashe kansu

A yayin da duniya ke bikin zagayoywar Ranar Hana Kisan Kai ta Dunai, bincike ya gano cewa akalla ’yan Najeriya 264 ne suka kashe kansu a cikin shekara hudu da suka wuce.

Adadin mutanen maza da matan da suka kashe kawunansu daga watan Janairun 2017 zuwa watan Agustan 2020 ya takaita ne ga wadanda kafafen yada labarai suka ba da rahotonsu. Taken bikin na bana  shin yin ‘Aiki tare domin dakile kashe kai’.

Kashe kai babban laifi ne a karkashin Sashe 327 na Dokar Manyan Laifuka a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

“Duk wanda aka samu da yunkurin kashe kansa ya aikata laifin da za a daure shi a kurkuku na shekara daya”, kamar yadda Sashen ya tanada.

– Abubuwan da ke sa kisan kai – 

Masana sun danganta yadda mutane ke kashe kawuwanansu da matsalolin kudi da na aure da sallama daga aiki da tsananin damuwa da sauransu.

Binciken Aminiya ya nuna Jihar Legas da ke yankin Kudu maso Yamma ce kan gaba, inda mutum 23 suka kashe kansu a tsawon lokacin.

Binciken ya nuna a watanni ukun farkon 2019 akalla ’yan Najeriya 42  ciki har da dalibai 11, sun kashe kansu ta hanyar shan maganin kwari ko guba ko kuma cinna wa kansu wuta.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasata cewa mutum 800,000 ne ke kashe kansu a duk shekara a fadin duniya.

Hakan na nufin mutum daya na kashe kansa a duk bayan dakika 40 a duniya.

Hukumar Dakile Kisan Kai ta Duniya (IASP) ta ce kisan kai shi ne abu na biyu da ya fi sanadiyyar mutuwar matasa ’yan shekara 15 zuwa 29 a duniya.

IASP ta ce kimanin mutum 30,000 na kashe kansu a duk shekara a kasar Amurka. Wasu mutum 650,000 kuma na samun kulawar gaggawa bayan sun yi yunkurin su kashe kansu.

WHO ta ce Najeriya ce kasa ta 30 a yawan mutanen da ke kashe kansu duk shekara a cikin kasashen duniya 183.

Ta ce kimanin kashi 17.1 ne cikin kowane mutum 100,000 ke yin hakan a shekara a Najeriya.

Kashi 78 cikin 100 na yunkurin kashe kai a duniya a shekarar 2015 sun auku ne a kasashe masu karanci da matsakaicin samu.

Kashi 1.4 cikin 100 na mace-macen da aka yi a 2017 sun faru ne ta hanyar kashe kai.

Najeriya ce kasa ta 10 a Afirka wurin yawan masu kashe kansu, sai kuma Togo (26), Saliyo (11), Angola (19), Burkina Faso (22).

Kasar Cote d’Ivoire ce ta biyar sannan Equatorial Guinea ita ce ta bakwai a jerin.